CIGABAN TARIHIN ANNABI ISAH (A. S)
Lokacin da suka ganta da goyo sai tace ku tambayeshi, sai suka ce yaya za'a yi mu tambaye shi alhalin gashi Yaro jariri karamin, bisa zanen goyo? Daga nan sai shi jaririn ya buda baki ya kar6a musu ya ce, ni bawan Allah ne Kuma Allah ya zakkeni mini da littafi ya kuwa Sanya ni in zama annabi, "" duk mutane kuwa suka rude, tsoro ya kamasu game da jawabin jaririn nan, Shugaban mu annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, Ana nan haka da Annabi Isah ya girma sai Allah madaukakin sarki ya aikowa da Annabi Isah annabi, ya aiko shi ga bani isra'ila ya zama Yana waazi ga umarnin da Allah ya aiko shi dashi, na cikin linjila. Jama'a suka yi ta karya tashi kamar yadda suka yi ta karyata annabawan da suka zo kafin shi, Ko Kuma su nuna abu mai wuya sauce shi suke so yayi musu su gani, in gaskiya ne Allah ne ya aiko shi, nan da nan sai Allah ya bashi iko yayi musu abin wannan , in sun gani sai suce sihiri ne ba muujiza bace ta annabci, ba wanda ya aiko shi! Hasali dai...