ANNABI ISAH (A. S) JESUS
Hasali dai, da yake tarihin annabi muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi. Muke Shirin bayarwa Bana dukkan annabawa ba sai mu dakatar a nan amma hakan ba yiwuwa Saboda yakamata mu bayaeda tarihin annabi Isah tunda shine mafi kusa da Annabi muhammadu tsira da Aminci su tabbata a gare shi,
Wato babban jigo ba Wato annabi Isah ruhullah.
A cikin dukkan manzannin Allah, Manzon sa annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, shine Manzo wanda yafi kusa da Annabi muhammadu tsira da Aminci su tabbata a gare shi, shi annabi Isah, Allah ya nufi mahaifiyarsa da Wato Maryama yardar Allah ta Kara tabbata a gare ta,
Maryam ta haifi annabi Isah ba tare da wani namiji ya kusanceta ba, madaukakin sarki Allah ya hukunta haka don ya nunawa yan Adam cewa, yadda yake iya Sanya mace ta haihu ba tare da wani ya kusan ce ta ba. Haka Kuma yakan Sanya namiji ya haihu ba tare da kusan tar mace ba, a wurin madaukakin sarki Allah wannan ba komai bane in ya so,
Haihuwar annabi Isah ba da uba ba, wata ayoyi ne daga cikin ayoyin ubangiji, kamar yadda ta bayyana a labarin annabawan baya.
To da mahaifiyar annabi Isah Wato maryamu ta dauki shi, suka kyalla IDO suka gan ta da da, ma'ana goyo sai suka ce cikin mamaki, daga ina kika samo jariri alhalin kuwa gaki baki da miji,
Comments
Post a Comment