CIGABAN TARIHIN ANNABI ISAH (A. S)

 Lokacin da suka ganta da goyo sai tace ku tambayeshi, sai suka ce yaya za'a yi mu tambaye shi alhalin gashi Yaro jariri karamin, bisa zanen goyo?

Daga nan sai shi jaririn ya buda baki ya kar6a musu ya ce, ni bawan Allah ne Kuma Allah ya zakkeni mini da littafi ya kuwa Sanya  ni in zama annabi, "" duk mutane kuwa suka rude, tsoro ya kamasu game da jawabin jaririn nan, Shugaban mu annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi,

Ana nan haka da Annabi Isah ya girma sai Allah madaukakin sarki ya aikowa da Annabi Isah annabi, ya aiko shi ga bani isra'ila ya zama Yana waazi ga umarnin da Allah ya aiko shi dashi, na cikin linjila.

Jama'a suka yi ta karya tashi kamar yadda suka yi ta karyata annabawan da suka zo kafin shi, Ko Kuma su nuna abu mai wuya sauce shi suke so yayi musu su gani, in gaskiya ne Allah ne ya aiko shi, nan da nan sai Allah ya bashi iko yayi musu abin wannan , in sun gani sai suce sihiri ne ba muujiza bace ta annabci, ba wanda ya aiko shi! Hasali dai har makaho aka kawo WA annabi Isah Allah ya bashi ikon mayar masa da ganinsa, ya bashi ikon warkar da mai ciwon daya buwayi magani, kai har matacce an kawowa annabi Isah Allah ya bashi iko ya mayar masa da ransa, amma duk da haka Jama'a da yawa basu yarda da shi ba a lokacin,

DA himmarsa ta iyar da sakon Allah ta tsananta sai yahudawa suka kulla makirci wai su kashe shi, aka kamo shi har aka zo dashi wurin da aka shirya za'a gicciye shi.

A an Allah madaukakin sarki ya nuna shine fiyayyen mai hikima, ya aikata Abinda ya aikata ya dauke shi zuwa sama,.

Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kubuta daga wannan kisa irin na wulakanci.

Anan zan takaita Labarin girman annabi Isah da yawan hikimomin ubangiji na gameda shi, annabi Isah ruhullah ya wuce ya bar mana wa'azin littafinsa mai tsarki linjila wanda ya tara zabura ta annabi dauda (A, S) da attaura ta annabi Musa (A, S) da busharar bayyanar annabi muhammadu tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

To bayan annabi Isah da shekara dari shida ne, Annabi muhammadu tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana Labarin shi shine zamu kutsa yanzu. 

Comments

Popular posts from this blog

To be continued PROPHET NUHU (AS)

THE PROPHET NUHU (A:S)